SiyasaAljeriya
Faransa na 'yar tsamar diplomasiyya da Aljeriya
April 15, 2025Talla
Ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta ce matakin da Aljeriyar ta dauka abin danasani ne, to amma tana duba hanyoyin warware kullin.
Sabanin Mali da Aljeriya na tasiri kan tsaron Sahel
Tun daga farko Aljeriyar ce ta ce ta dauki matakin a matsayin martani kan tiso keyar wasu jami'an diflomasiyyarta daga birnin Paris, inda ta bukaci ma'aikatar harkoklin wajen Faransa da ta janye, sai dai kuma ta yi biris da ita.
Nijar da Faransa an raba gari kwata-kwata
Wannan sabuwar takaddamar diplomasiyyar da ta barke a tsakanin Faransa da Alejriya na zwa ne kwanaki bayan wata ziyarar aiki da ministan harkokin wajen Faransar ya kai a kasar Alejriya da zummar kara inganta dangantaka a tsakaninsu.