Faransa ta musguna wa Kamaru - Macron
August 13, 2025Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya amince cewa kasarsa ta musguna wa al'ummar Kamaru a lokacin da ta yi mata mulkin mallaka har zuwa samun 'yancin kai a tsakanin shekarun 1950.
Macron ya fadi haka ne a wata wasikar da ya fitar wacce ta kunshi irin jerin abubuwa da Faransa ta aikata a Kamaru kuma aka wallafa wasikar a ranar Talata.
Tsofaffi sun mamye siyasar Afirka
Wasikar, wacce aka tura wa takwaransa na Kamaru a watan da ya gabata, na daga cikin sabbin misalan yadda Faransa a karkashin Macron ke kokarin fito da abubuwa da suka faru yayin mulkin mallakar da ta yi.
Amincewar ta biyo bayan wani rahoto ne da aka wallafa a hukumance a watan Janairu, wanda ya ce Faransa ta tilasta wa jama'a da yawa yin hijira.
Kamto ya yi tir da watsi da takararsa a zaben shugaban kasa
Wasikar ta kuma amince cewa Faransa ta tura dubban 'yan Kamaru sansanonin gwale-gwale tare da goyon bayan kungiyoyin ‘yan bindiga domin murkushe yunkurin neman ‘yancin kai na kasar.