Faransa ta mika sansanonin sojinta na karshe ga Senegal
July 17, 2025Matakin fadar Elissee ya kawo karshen zaman dakarun Faransa a kasar Senegal na tsawon shekaru 65, biyo bayan raba gari da kasashen da Faransar ta yi wa mulkin mallaka suka yi mata a nahiyar. Ficewar sojojin na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen Burkina Faso da Mali da kuma Jamhuriyar Nijar ke fuskantar kalubale mafi girma na masu ikirarin jihadi da ke dauke da muggan makamai.
Karin bayani: Ko ana iya rufe babin Faransanci a nahiyar Afirka?
An dai gudanar da kwarya-kwaryar bikin mika barikin sojojin Geille da kuma na sansanin sojin saman Paris da ke filin jiragen sama na birnin Dakar, a gaban wakilan kasashen biyu da suka hadar da shugaban hafsan sojojin Senegal Janar Mbaye Cisse da kuma Janar Pascal Ianni, shugaban dakarun Faransa a Afirka.