SiyasaVatican
Fafaroma Leo XIV ya fara aiki a hukumance
May 18, 2025Talla
Dubun dubatar mutane ne za su isa dandalin St Peters, ciki kuwa har da gomman shugabanin kasashen duniya da manyan shugabannin addini da kuma sarakuna, yayin da Fafaroma Leo XIV ke fara aikin shugabancin darikar Katolika. Ana sa ran yayin bikin, Fafaroma Leo zai zagaye filin a motarsa ta Fafaroma bayan kwanaki 10 da zabensa domin maye gurbin marigayi Fafaroma Francis da ya mutu a ranar 21 ga watan Afrilun wannan shekarar.
Karin bayani: Fafaroma na samun sakonnin taya murna daga duniya
Tun daga jawabinsa na farko bayan an zabe shi, ake ganin Fafaroma Leo zai mayar da hankali a kan zaman lafiya tare da dorawa daga inda marigayi Fafaroma Francis ya tsaya a wannan fannin.