Fafaroma Leo na Katolika ya ce a yi wa Gaza da Ukraine azumi
August 21, 2025Jagoran darikar Katolika na duniya FafaromaLeo na 14, ya yi kira da a tashi da azumi ranar Juma'a, don neman agajin mahalicci wajen samun wanzuwar zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya da kuma Ukraine.
Fafaroma Leo ya bukaci hakan yayin taron ibada na musamman ranar Laraba, yana mai jaddada muhimmanin yin azumi da addu'o'i ranar Juma'a da ubangaji ke amsa rokon bayinsa, kamar yadda yake cikin koyarwar addinin kirista.
Sannan ya nemi a koma kan teburin tattaunawar sulhu tsakanin bangarorin da ke yaki da juna, don samar da masalahar da za ta kai ga tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Gaza da Ukraine.
Karin bayani:Qatar da Masar na jiran ra'ayin Isra'ila kan yakin Gaza
Shi ko sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya nemi a gaggauta kawo karshen yakin Gaza, don kauce wa asarar rayuka da dukiyoyin da za a fuskanta nan gaba, bayan da Isra'ila ta ayyana shirinta na matakin farko na kwace ikon Gaza.
Mr Guterres na wannan jawabi a wannan Alhamis, yayin taro na musamman a birnin Tokyo na kasar Japan, kan bunkasa kasashen nahiyar Afirka, yana mai jan hankalin hanzarta tsayar da yakin haka, don tseratar da rayukan Falasdinawan Gaza da ke shan luguden wutar sojojin Isra'ila.
Ya kara da cewa yunkurin na Isra'ila ya sabawa dokokin kasa-da-kasa da kudurorin Majalisar Dinkin Duniya.
Karin bayani:Kasashen duniya na son kawo karshen yakin Ukraine
Tuni Isra'ila ta ayyana fara aiwatar da mamayar Gaza baki-daya ta karfin tsiya, inda ta yi gangamin dakarun sojinta na musamman dubu sittin da za su aiwatar da shirin.