Fafaroma ya yi addu'ar Easter duk da rashin lafiya
April 20, 2025Zaune akan keken masu larurar kafafu tare da nuna alamu na jin jiki, Fafaroma Francis ya isar da sakon Urbi - Orbi ga mabiya darikar fiye da biliyan daya da miliyan 400 a duniya.
Fadar Vatican ta karbi bakuncin mataimakin shugaban Amurka
A cikin jawabinsa da aka karanta, Jagoran na Khatolikan mai shekaru 88 ya caccaki yanayin da ake jiki na tabarbarewar ayyukan jin-kai a Zirin Gaza, tare da kira ga bangarorin biyu na Hamas da Isra'ila da su daidaita domin sako wadanda ake garkuwa da su da dakatar da yaki don shigar da kayan agaji.
Paparoma Francis ya fito bainal jama'a
Ba'idinsa jagoran na mabiya Addinin Kirista, ya bayyana cewa ba wani cikakken zaman lafiyar da za a iya samu madamar ba a mutunta 'yancin yin addini da na walwala da 'yancin bayyana tunani ba a duniya.
Paparoma Francis ya caccaki Trump
Tun gabanin fitowarwa, fadar Vatican ta sanar da cewa Fafaroma Francis ya gana da mataimakin shugaban Amurka JD Vance na wani dan takaitaccen lokaci, watanni bayan da Fafaroma Francis ya caccaki manufofin shugaban Amurka Donanld Trump na korar 'yan ci-rani a kasar.