SiyasaJamus
Fafaroma Francis ya bar asibiti
July 14, 2021Talla
Rahotannin da ke fitowa daga Italiya, na cewa jagoran darikar Katholika na duniya Fafaroma Francis, ya koma fadar Vatikan bayan kwashe kwanaki 10 a asibiti sakamakon wani aikin fida da aka yi masa.
Masu aiko da rahotanni sun ce Fafaroma Francis mai shekaru 84, ya ma tsaya a majami'ar St. Mary Basilica ya kuma yi addu'o'in godiya da nasarar da aka samu a tiyatar da aika yi masa.
A shekara ta 2013 a lokacin da ya zama Fafaroma, an yi wa jagoran na Katholika na duniya aiki a 'ya'yan hanjinsa, inda bisa shawarar kwararru aka tsara ta wannan lokaci.
Yanzu dai Fafaroma Francis zai kwashi wasu 'yan makonni kafin komawa harkokinsa, inda bayanai ke cewa zai ziyarci kasashen Hangari da Slovakia cikin watan gobe na Satumba.