Fadar White House ta kaddamar da shafinta na TikTok
August 20, 2025Fadar gwamnatin Amurka ta White House ta kaddamar da shafinta na TikTok a hukumance a ranar Talata, a daidai lokacin da dandalin sada zumuntar mallakin China ke fuskantar barazanar haramci a Amurkar.
Sa'o'i uku bayan wallafa bidiyo na farko, shafin na White House ya samu mabiya sama da 25,000 yayin da shafin Donald Trump ke da mabiya sama da miliyan 110 duk da cewa shugaban bai wallafa komai ba tun ranar biyar ga watan Nuwamban bara.
Karin bayani: Trump ya bukaci jinkirta haramcin amfani da TikTok
A shekarar 2024 ne dai majalisar dokokin Amurka ta amince da wata doka da ta jibanci haramta dandalin sada zumuntar na TikTok mai matukar tasiri a Amurka idan ba a sayar wa kasar da shi ba, saboda fargabar cewa China na iya amfani da wannan kafa domin yin kutse ga bayanan hukuma ko kuma sauya tunanin Amurkawa. To sai dai shugaba Donald Trump ya daga kafa ga aiwatar da wannan doka har i zuwa ranar 17 ga watan Satumba mai kamawa.