Shirin fadada sufurin jiragen kasa
January 23, 2025'Yan tawayen M23 a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango na ci gaba da karbe yankunan kasar. A ranar Talata sun kwace garin Minova da ke gabashin kasar sannan suka kutsa suka kwace iko da daya daga cikin manyan hanyoyin samar da kayayyaki ga babban birnin lardin Goma.
Matsalar tsaro a yankin na ci gaba da tabarbarewa sakamakon yadda 'yan tawaye ke kara mamaye yankunan. Tun shekara ta 2022 kungiyar M23 da Tutsi ke jagoranta take sake tsunduma cikin yaki bayan yarjejeniyar lafiya ta warware. Kwararru a Kongo da Majalisar Dinkin Duniya suna zargin makwabciyarta Ruwanda da tallafa wa kungiyar da dakarunta. Amma Rwanda ta musanta hakan.
Karin Bayani: Gabashin Jamhuriyar Demokaradiyya Kwango cikin halin yaki
Kamar yadda aka sani akwai tayin da gwamnatin Amurka mai barin gado ta yi na shigar da yankin da ake yaki a gabashin Kongo cikin wani gagarumin aikin samar da ababen more rayuwa.
An bai wa bangarorin biyu damar daidaita yankin gabas tare da yin aiki kan bunkasa zirga-zirga ta hanyar Lobito sashen da ke a gabashin Kongo, a cewar Molly Phee, tsohon mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka a wata hira da kamfanin dillancin labarai na AFP.
Manufar gwamnatin Amurka ita ce ta samar da hanyar karfafa gwiwa don warware rikicin. Amma a halin yanzu da alama Ruwanda ta fice daga wannan shiri, Shugaban Rwanda Paul Kagame bai halarci tattaunawar da Angola ta shiga tsakani ba don tattaunawa da shugabannin kasashen Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, da Zambiya da Tanzaniya a ziyarar da shugaban Amurka na wancan lokacin Joe Biden ya kai Angola a watan Disambar na shekara ta 2024.
A watan Yunin na shekara ta 2024, gwamnatocin biyu na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da Ruwanda suka amince za su yi shirin tsawaita hanyar sufuri daga Isaka dake a Kwango zuwa Kigali.
Hanyar Lobito ta ƙunshi layin dogo mai tsawon kilomita 1,300 daga tashar jiragen ruwa na Lobito da ke gabar tekun Atlantika zuwa Angola zuwa garin Luau da ke kan iyakar Angola da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango zuwa garin Kolwezi, kusa da arewa maso yammacin kasar. Zambiya.
Layin dogo ya ja har tsawon kilomita 400 zuwa cikin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango zuwa garin Kolwezi inda ake hakar ma'adinai. Daga can ana son a gaggauta safarar ma'adanai irin su cobalt da tagulla da kuma dakile tasirin kasar Chaina a yankin, kamar yadda kasashen Turai da Amurka masu ba da kwangila suka bayyana, saboda kasar Chaina ce ta mamaye fannin hakar ma'adinai a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da Zambiya.