EU za ta yi wa shugaba Trump na Amurka martanin karin haraji
April 3, 2025Kungiyar tarayyar Turai EU ta ce karin harajin kayayyakinta na kashi 20 cikin 100 da shugaba Donald Trump ya yi wa hajojinta da ke shiga Amurka, wani gagarumin koma-baya ne ga tattalin arzikin duniya da zai gurgunta sha'anin kasuwanci.
Shugabar hukumar tarayyar turai Ursula von der Leyen ta ce karin harajin zai yi mummunan tasiri ga miliyoyin marasa karfi a duniya, sakamakon tashin farashin kayan masarufi da tafiye-tafiye, har da na harkokin kiwon lafiya da za a fuskanta.
Karin bayani:Shugabannin kasashe da gwamnatocin kungiyar Tarayyar Turai su 27 za su tattauna
Ta kara da cewa a shirye suke su mayar da martani ga matakin Mr Trump daidai da abin da ya aikata, to amma kofarsu a bude take domin tattauna yarjejeniyar daidaita wa.
Karin bayani:EU ta cewa Isra'ila tilas a mayar da al'ummar Gaza gida
Kasashen duniya da dama sun mayar da martani kan karin harajin na Mr Trump, wanda ya fara aiki a wannan Alhamis.