EU ta nemi a koma tattauna shirin nukiliyar Iran.
July 1, 2025Babbar jami'iar diflomasiyyar kungiyar tarayyar Turai Kaja Kallas ta shaidawa ministan harkokin kasashen ketare na Iran Abbas Aragchi cewar Brussels a shirye take ta shige gaba don ganin an koma teburin tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran bayan hare-haren Amurka a tashoshin makamashinsu.
Bayan wata doguwar tattaunawa ta wayar tarho da jami'ar ta yi da Mista Argchi, ta wallafa a shafinta na X cewar ya kamata a koma tattaunawa kan makamashin Iran cikin gaggawa, kuma akwai bukatar hadin kai daga hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa domin cimma yarjejeniya.
Kazalika Kallas ta gargadi Tehran cewar duk wani yunkuri na janyewa daga tattaunawar ka iya dagula al'amura.
Wannan na zuwa ne bayan da Tehran ta yi watsi da sake komawa kan teburin tattaunawa da hukumar ta yi, inda Tehran ta ce tana bukatar tabbacin Amurka ba za ta sake kai mata hari ba.
A baya dai kungiyar EU ta kasance mai shiga tsakani a yarjejeniyar nukiliyar Iran na 2015 da aka cimma da manyan kasashen duniya, kafin daga bisani Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi watsi da yarjejeniya a shekarar 2018.
Karin Bayani:Shugaban IAEA ya ce Iran na daf da mallakar makamin nukiliya