EU za ta je Isra'ila kan sabbin hare-hare a Gaza
March 23, 2025Talla
Ofishin jami'ar ta Turai ya sanar da haka a wannan Lahadi, yana mai cewa a yayin ziyarar, Kallas, za ta tattauna rikicin Gaza, ta tunasar da bangarorin da abin ya shafa muhimmancin bude kofar shigar dakayan agaji a Zirin Gazada hanzarta dawo da aiwatar da yarjejeniyar sakin fursunonin siyasa da dakatar da kai hare-hare.
Jami'ar za ta tattauna da ministocin Isra'ila da na Falasdinu domin shawo kan sabon rikicin da ya sake kaurewa a makon nan bayan harin da Isra'ila ta kai.
MDD ta ce Zirin Gaza ya shiga cikin mawuyacin hali tun bayan sabbin hare-haren da Isra'ila ta dawo da su bayan makonni shida da aka kwashe ana aiki da tsagaita wuta.