EU ta wallafa rahoto game da zaɓe a Nijar
June 2, 2011Tawagar ƙungiyar Tarayya Turai da ta sa ido ga zaɓɓuɓuka dabandaban da su ka gudana a jamhuriyar Nijar a wannan shekara ta 2011, ta yi yabo ga hukumar zaɓe mai zaman kan,ta da gwamnatin riƙwan ƙwarya da kuma al'umar Nijar game da yadda aka shirya zɓben cikin tsafta da haske.
A ɗaya hannun kuma EU ta bada shawarwari ga magabatan Nijar da zumar zuwa gaba a ƙara inganta harkokin zaɓe a ƙasar.
To saidai a halin da ake ciki kuma, an shiga wata cece kuce game da albashin 'yan majalisar dokoki, inda wasu ƙungiyoyin farar hula suka yi ƙorafin cewar yan majalisar sun yi wa kansu raban kura, ta hanyar ware albashi mai yawa.
Za ku ji duk wannan a cikin rahotannin da wakilanmu na Yamai Gazali Abdou Tasawa da Mahaman Kanta su ka aiko mana.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mohammad Nasiru Awal