EU ta kakabawa sojojin Ruwanda da 'yan tawayen M23 takunkumi
March 17, 2025Takunkuman na kungiyar EU sun shafi wasu manyan kwamandojin sojin kasar Ruwanda da kuma wasu manyan shugabannin 'yan tawayen M23, kazalika an kuma laftawa gwamnan Kivu ta arewa na shi takunkuman.
Kungiyar tarayyar Turai wacce tagargadi bangarorin biyu a kan kisan fararen hula ta ce dole ne a kawo karshen wannan rikicin dake ci gaba da lakume rayukan al'umma.
Sama da mutane 7000 ne suka mutu tun daga farkon watan Janairun wannan shekara kawo yanzu a yakin da ake gwabawa tsakanin 'yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Ruwanda da kuma sojojin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango.
A kokarin kawo karshen wannan rikicin, kungiyar M23 dake samun goyon bayan Rwanda ta zargi gwamnatin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango da neman ruguje tattaunawar zaman lafiya da ake kokarin a cimma.
Karin Bayani:Mai ya hana kawo karshen rikicin Kwango?