EU na yunkurin farfado da hulda da Jamhuriyar Nijar
February 18, 2025Tawagar kungiyar ta EU da ta isa birnin Yamai ta fara ne da ganawa da firaministan kasar Mahaman Ali Lamine Zeine a fadarsa . Bangarorin biyu sun tattauna muhimman abubuwan da ya kamata su mayar da hankali a kansu a sabuwar huldar da suke son kullawa a tsakaninsu bayan zaman doya da manja na tsawon watanni a sakamakon juyin mulki. Kuma a karshen ganawar, Soao Cravinho da ke zama sabon wakilin musamman na kungiyar ta EU a Sahel ya yi Karin haske kan shirin.
Karin bayani: Sabuwar takaddama tsakanin sojojin Nijar da kungiyar EU
Soao Cravinho ya ce: "Kyakkyawar huldar da aka dora min nauyin samarwa tsakanin Nijar da Kungiyar Tarayyar Turai, hulda ce da ke bukatar a gina ta a kan fahimtar juna. Kuma wannan na bukatar sauraren juna, domin muna da babban buri ga kasar Nijar a nan gaba. Don haka akawai bukatar mu zauna tare, mu tantance abubuwan da ke da muhimmanci ga kowane daga cikin bangarorin biyu. Lallai abu ne da ke bukatar hakuri da kuma lokacin da juriya, amma duk da haka a shirya muke mu yi wannan hulda. Da mu kungiyar EU da mahukuntan Nijar ,kowanen mu na son wannan hulda. Don haka komai zai tafi daidai."
Bambancin ra'ayi kan huldar EU da Nijar
Shekaru da dama ne dai kungiyar Tarayyar Turai ta shafer tana taimaka wa Nijar a fannonin inganta rayuwar al'umma da ayyukan raya kasa. Sai dai a yayin da wasu ‘yan kasar Nijar ke nuna gamsuwarsu da matakin kungiyar ta EU na kyautata hulda da Nijar, wasu ‘yan kasar na cewa akwai bukatar mahukunta su yi taka tsan-tsan a sabuwar tafiyar. Saboda haka ne Soule Oumarou Na Kungiyar FCR yake ganin alkhairi ne ci-gaba da wannan hulda da kuma kyautata ta , ta yadda za ta yi daidai da sabuwar tafiyar Nijar: Sai dai Soly Abdoulaye, wani dan fafutika na ganin cewar kungiyar ta EU na neman cimma muradenta ne.
Karin bayani:Nijar ta soke kawancen tsaro da EU
A watan Nowamban 2024 ne, kungiyar Tarayyar Turai ta nada Soao Cravinho a matsayin sabon wakilinta na musamman a yankin Sahel da nufin tabbatar da tsaro da zaman lafiya da samar da ci-gaba mai daurewa a yankin, wanda ya kunshi kasashen Chadi da Moritaniya da kuma Jamhuriyar Nijar Mali da Burkina Faso wadanda huldasu da kungiyar ta raunana a sakamakon juyin mulki da sojoji suka yi.