EU da Japan za su yi aiki tare don sauya tsarin kasuwanci
July 23, 2025Shugabar kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta shaida wa manema labarai a birnin Tokyo cewar a duniyar yau, dole ne a gina gasa tare da amintattun abokan hulda irin su Japan, duba da yadda tare Turai da Japan suna wakiltar kashi biyar na tattalin arzikin duniya.
Yayin da yake fuskantar cece-kuce game da makomarsa bayan rikicin zaben karshen mako, Framinista Ishiba Shigeru ya ce EU da Japan sun amince da yin aiki tare don karfafa a bun da ya kira "tsayayyen tsari da za a iya hasashen ka'idojin tattalin arziki mai 'yanci da adalci".
Brussels da Tokyo sun ba gabatar da wannan sanarwa ne a wani taro a babban birnin Japan, inda Von der Leyen ta taya firaministan murna kan nasarar tattaunawar don cimma yarjejeniyar haraji da Washington.