Elon Musk ya kaddamar da jam'iyya a Amurka
July 6, 2025Attajiri Elon Musk wanda ya bayyana hakan ne a dandalinsa na sada zumunta na X, ya ce manufar wannan jam'iyya ita ce ta dawo wa da ‘yan Amurka ‘yancinsu.
Wannan sabuwar jam'iyya ta zo ne dai bayan Elon Musk ya samu sabani da shugaban kasa Donald Trump, musamman game da dokar haraji da kashe kudade masu yawa da Trump ya amince, wadda kuma Mista Musk ya yi suka sosai a kai.
Attajirin da ya shiga harkokin siyasa dumu-dumu ya yi alkawarin kafa wannan jam'iyya ne domin kalubalantar ‘yan jam'iyyar Republican da suka goyi bayan wannan doka, wadda ake ganin za ta kara bashin kasar Amurka da yawa.
A kasar Amurka jam'iyyun siyasa biyu ne suka mamaye fagen siyasa, wato da Democratic Party da kuma Republican Party.
Shi dai Elon Musk ba shi ne mutum na farko da ya yi kokarin karya tsarin jam'iyya biyu ba; a shekarar 1912, tsohon shugaban kasa Theodore Roosevelt ya yi kokarin kafa jam'iyyar Progressive Party inda ya samu kaso mai yawa na kuri'u, amma kuma bai lashe zabe ba