El-Rufai na shirin yamutsa hazon siyasar Najeriya a 2027
March 11, 2025Bayan da tsohon gwamman jihar Kaduna Nasir El-Rufa'i ya kwashe tsawon lokaci yana ganawa da jiga-jigan 'yan adawa a Najeriya ne ya yar da kwallon mangwaron da ya fara doyi a hannunsa domin ya rabu da kuda. Kafin wannan mataki, sai da ya yi wa tsohuwar jam'iyyarsa da ke mulki wankin babban bargo kafin a yanzu ya koma jam'iyyar adawa ta SDP. Fitar El-Rufai ya kama hanyar sauya siyasar Najeriya musamman a jam'iyyar APC, sanin matsayinsa a fagen siyasar Najeriyar da ba za' iya saurin kau da kai a kansa ba.
E-Rufai ba ya shayin bayyana ra'ayinsa na siyasa
Mallam Nasir El-Rufai dai dan siyasa ne mai kaifin baki wajen bayyana ra'ayinsa, domin ko da manyan jam'iyyun adawa guda biyu na PDP da Labour bai raga masu ba, duk da yunkurin samar da hada kan jam'iyyun adawa a Najeriya. Sai dai, duk da kokari,El-Rufai na sauya akalar siyasar Najeriya a 2027, amma fadar shugaban Najeriya ta bayyana cewa ba ta girgiza ba. Amma Dr Kabiru Danladi Lawanti, mai sharhi kan al'amuran yau da kullum ya ce tarihi zai iya maimaita kansa kamar yadda ya faru a 2013.
Mafarkin hadewar jam'iyyun adawa a Najeriya
Daya daga cikin 'yan siyasa da suka yi gaba kafin ficewar El-Rufai kamar Salihu Lukman ya bayyana cewa tsohon gwamnan ya yi hanzari domin akwai gungu da ke shirin ficewa daga jam'iyyar ta APC don kafa wata babbar jam'iyyar adawa. A baya dai, an ga irin wannan a lokacin da tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ke mulki da ya samu bijerewa daga wasu 'yan arewacin Kasar, kamar yadda ya fara faruwa ga mulkin Bola Tinubu. Wasu 'yan siyasa da masu fashin baki na hasashen cewa shiga jam'iyyar SDP da El-Rufai ya yi zai iya kawo cikas a shirye-shirye da wasu gaggan 'yan siyasa ke yi na kafa wata babbar jam'iyyar adawa a Najeriya.