Ekrem Imamoglu zai tsaya takarar shugaban kasa a Turkiyya
March 23, 2025Babbar jam'iyyar adawa a kasar Turkiyya Republican People's Party CHP, za ta gudanar da zabenta na cikin gida a wannan Lahadi, wanda ake sa ran za ta fitar da magajin garin Santambul da yanzu haka ke tsare Ekrem Imamoglu a matsayin 'dan takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa.
Karin bayani:Turkiyya: Imamoglu ya lashe zaben Magajin Garin Santanbul
Jam'iyyar mai mambobi miliyan daya da rabi, za ta ajiye akwatunan zabe dubu biyar da dari shida a larduna 81 na kasar, inda za a fara jefa kuri'a da karfe biyu na rana agogon GMT.
Gwamnatin kasar ta cafke Ekrem Imamoglu bisa zargin cin hanci da rashawa da tallafawa 'yan ta'adda, wanda tuni ya musanta aikata hakan.
Karin bayani:Erdogan ya nemi a kakaba wa Isra'ila takunkumi kan makamai
Za a gudanar da zaben shugaban a Turkiyya a cikin shekarar 2028.