Me EFCC ta binciko a farfajiyar dakin karatu na Obasanjo
August 11, 2025Wannan ne karon farko da jami'an hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriyar EFCC suka yi ta maza inda suka yi wa otel din da ke a farfajiyar dakin karatu na tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo da ke garin Abeokuta bincike. Sun cafke matasa 93 da suke zarginsu da zamba cikin aminci ta yanar gizo da wasu dilallan motocin da aka samu a wajen.
Tuni wannan ya sanya musayar kalamai a tsakanin dakin cibiyar karatun ta Obasanjo da hukumar ta EFCC. Mr Dele Oyewale shi ne kakakin hukumar mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya:
‘' Mun cafke mutane 93 ne a wani otel a garin Abeokuta mu; ba mu ambata ko Otel din Franklin ko na Dele ba ne, mun ce a Abeokuta ne kuma da gangan muka yi haka. Wadannan mutane da muka kama muna nan muna bincike a kansu idan muka kammala za mu gabatar da su da ma abubuwan da muka gano tare da su''.
Ko da yake ra'ayoyin sun sha bamban a kan yadda ake kalon wannan kame da hukumar taEFCC ta yi, sanin matsayin tsohon shugaban Najeriyar Olusegun Obasanjo da wasu ke danganata lamarin da siyasar Najeriyar da guguwarta ke kadawa.
Tuni hukumar gudanarwar dakin karatun tsohon shuagban na Najeriya ta yi barazanar za ta dau matakin shari'a a kan hukumar ta EFCC wacce ke kaucewa fito na fito da tsohon shugaban na Najeriya, To sai dai ga Dr Umar Yakubu kwararre a fanin yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya wanda shi ne shugaban kungiyar kamanta gaskiya da adalci na bayyana yadda yake kalon wannan lamari:
''Matsalar zamba cikin aminci ta yanar gizo na cikin babban kalubalen da ake fuskanta musamman a tasakanin wasu matasan Najeriyar da ke son arzikin dare daya ta hanyar yaudarar mutane da dama, matsalar da ta faro daga kasashen da dama, abin da ya sanya hukumar ta EFCC baza komarta inda take cafko masu wannan hali ta hadin guiwa da hukumomin kasa da kasa.