ECOWAS ta koka da munin matsalolin tsaro a yammacin Afirka
June 23, 2025Jagororin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS, sun amince da cewa yankin ya tsunduma cikin mummunan yanayi na tashe-tashen hankula da rikice-rikicen siyasa.
Sabon shugaban kungiyar kuma shugaban kasar Saliyo Julius Maada Bio ne ya tabbatar da hakan, yayin taron da kungiyar ta gudanar ranar Lahadi, a Abuja fadar mulkin Najeriya, lokacin da ya karbi jagorancin kungiyar na karba-karba, daga hannun takwaransa na Najeriya Bola Tinubu.
Karin bayani:ECOWAS da AES sun fara girmama juna a huldar kasa da kasa
Shugaban ya zayyano matsaloli irin su hare-haren ta'addanci musamman a yankin Sahel da tafkin Chadi, da na 'yan bindiga, sai safarar makamai da juyin mulkin sojoji, da ma sauran miyagun ayyuka, da ya kamata a kawo karshensu.
Julius Maada Bio ya koka da munin halin da kasashen Mali da Burkina Faso da kuma Jamhuriyar Nijar ke ciki, na fuskantar kazaman hare-haren ta'addanci a baya-bayan nan.