ECOWAS da AES sun fara girmama juna a huldar kasa da kasa
May 23, 2025A yayin tattaunawar ta birnin Bamako, bangarorin biyu sun tattauna muhimman batutuwan da suka shafi siyasa, diflomasiyya, shari'a, tsaro da ci-gaban tattalin arziki. Sannan sun duba batun zamantakewa da ba da fifiko ga moriyar al'ummar yammacin Afirka ta hanyar kiyaye nasarorin da aka samu a baya, musamman na zirga-zirgar jama'a da dukiyoyinsu cikin 'yanci har zuwa lokacin da bangarorin biyu za su kulla sabbin yarjejeniyoyi. Masu sharhi na yi wa wanna zama na farko kallon wani abu mai cike da nadama ko darasi, kamar yadda Dr Atto Namaiwa, malami a jami’ar Birnin Tahoua, mai sharhi kan harkokin yau da kullum a yankin yammacin Afirka ya bayyana.
Karin bayani: Wakilan Kungiyar AES na tattaunawa kan manufofin kungiyar
Mahalarta na kungiyar ECOWAS da AES sun bayyana damuwarsu game da lamarin tsaro da ke addabar kasashe da dama na yammacin Afirka tare da cimma matsaya kan gaggawar yin aiki tare don samar da tsari da yanayin da ya dace ta yadda za a samu ingantaccen hadin gwiwa don yakar ayyukan ta'addanci a yankin na yammacin Afirka. Wannan shi ne ra'ayin Omar Souley, shugaban kungiyar farar hula FCR da ke fafutukar kare hakkin jama’a da ci gaban dimukuradiyya.
Karin bayani: Martanin 'yan NIjar kan ficewar AES daga ECOWAS
Bangarorin biyu na AES da ECOWAS sun jinjina wa juna kan yadda wannan zama ya wakana a yanayi na 'yan uwantaka a wannan mu’amula ta farko da ta gudana kai tsaye tare da amincewa da ci gaba da irin wannan tattaunawa, da saka bukatun al'ummomin yammacin Afirka a gaba. Soumaila Amadou, dan siyasa kuma mai sharhi kan zamantakear al’umma ya yi tsokani. Inda yake cewa mataki ne mai kyau.
Karin bayani: Kasashen ECOWAS sun ragu
Ana jiran ganin muhimman matakan da bangarorin biyu na ECOWAS/CEDEAO da AES za su dauka da batun yarda da juna, idan aka yi la’akkari da bambancin da ke tsakanin bamgarori biyu dangane da batun samun cikakken 'yancin kai daga Turawan mulkin mallaka.