SiyasaAfirka
Ebola ta halaka mutane 15 a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango
September 4, 2025Talla
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta tabbatar da mutuwar mutane 15 a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, sanadiyyar kamuwa cutar Ebola.
Rahoton WHO na zuwa ne bayan da hukumomin lafiyar kasar suka tabbatar da barkewar annobar zazzabin na Ebola a lardin Kasai, inda mutane 28 suka kamu da cutar.
Karo na 15 kenan da Kwango ke fuskantar barkewar annobar cutar Ebola, tun bayan gano ta a karon farko a shekarar 1976 a kasar.
Karin bayani:Ana zargin bullar cutar Ebola a Jamhuriyar Czech
Alamunta sun hada da zazzabi mai zafi da ciwon makogwaro da zubar jini da amai da gudawa da kuma ciwon jiki.