Durkushewar kamfanoni a kasashen yammacin Turai.
February 4, 2004Talla
A cikin wannan shekarar ma za´a ci-gaba da fuskantar matsalar ta durkushewar kamfanoni musamman a nan Jamus. Duk da alamun farfadowar tattalin arzikin kasar kuwa, a bana yawan kamfanonin Jamus da zasu talauce zai kai dubu 42. Dalilin haka kuwa shine rashin ciniki da kuma karancin kudi da abokan huldar cinikin su ke fuskanta. Shugaban kungiyar ba da rance ta Creditreform Helmut Rödl ya nuna wannan halin da ake ciki da cewa abin damuwa ne, amma duk da haka kamfanonin Jamus da na sauran kasashen yammacin Turai na fatan farfadowar tattalin arzikin zai taimakawa harkokinsu na ciniki. Dalilin da yasa a bana ma kamfanonin musamman kanana da matsakaita zasu durkushe shine rashin samun rance daga bankuna don tafiyar da aiki.
A bara yawan kamfanoni da suka durkushe a kasashen yammacin Turai ya kai dubu 157, sannan kasashen Jamus da Faransa ke kan gaba da kamfanoni dubu 39, yayin da aka yi asarar guraben aikin yi miliyan 1.7 a duk fadin nahiyar Turai. Kimanin kashi 15 cikin 100 na marasa aikin yi na da dangantaka da durkushewar kamfanoni. A Jamus kadai mutane kimanin dubu 613 suka yi asarar wuraren aikinsu a cikin shekarar da ta wuce, wato an samu karin marasa aikin yi dubu 23 idan aka kwatanta da bara waccan. Haka zalika hakan ya jawo asarar kudaden shiga sama da Euro miliyan dubu 40. Duk hasashen da aka yi na nuni da cewa kanana da matsakaitan kamfanoni zasu fi fadawa cikin mawuyacin hali na rashin kudi, domin sabbin dokokin da aka kafa na kawo babban cikas ga kamfanonin da ba su da isasshen jarin kansu wajen samun rance. Yanzu haka dai sama da kashi 90 cikin 100 na wadannan kamfanonin sun dogara ne da rancen da suke samu daga bankuna, saboda haka da zarar wannan hanyar ta toshe, to ba su da zabi face su rufe kamfanoninsu.
Duk da wannan matsala da ta zama ruwan dare a nahiyar Turai, wasu kasashe kamar na yankin Skandinaviya, sun samu bunkasar ciniki a cikin shekarar da ta wuce. A kasar Britaniya da jamhuriyar Ireland ma an samu raguwar kamfanonin da ke durkushewa. Haka zalika alkalumman da kasashen Poland da Slovakiya da Lithuaniya, wadanda za´a dauke su cikin kungiyar EU a cikin wannan shekara, suka bayar yayi nuni da raguwar yawan kamfanoninsu dake talaucewa, yayin da a kasar Hungary kuwa aka samu karin kashi daya cikin hudu na kamfanonin da suka durkushe.

Talla